Labarai
CBN ya gargadi bankuna kan kyautatawa abokan hurda
Babban bankin kasa (CBN), ya gargadi bankunan kasuwanci na kasar nan da su gaggauta warware matsalolin da abokan huldarsu masu amfani da na’urar cirar kudi ta ATM ke fuskanta, cikin watanni ashirin da hudu.
A cikin wata sanarwar da bankin ya fitar a jiya lahadi, ya ce, daga yanzu maimakon bankunan su rika kwashe tsawon kwanaki uku, idan abokan huldarsu sun fuskanci matsalar (ATM), yanzu dole ne a magance matsalar cikin wa’adin kwana guda kacal.
CBN: zai janye kudaden da suka lalace daga hannu jama’a
Covid19: Bankin CBN ya bayyana ka’idojin bayar da tallafi
A cewar sanarwar ta bankin CBN wannan doka za ta fara aiki ne a ranar takwas ga wannan wata da muke ciki na Yuni.
Haka zalika sanarwar ta kara da cewa, matsaloli da abokan huldar bankunan ke fuskanta, wadda a wasu lokutan mutum zai ciri kudi daga asusun ajiya, amma kuma na’urar ba ta bashi kudin ba, to dole ne a dawo mishi da kudin cikin wa’adin awanni arba’in da takwas, maimakon kwanaki uku ko biyar da ake yi a baya.
Bankin na CBN ya kara da cewa matukar matsala ta shafi masu amfani da na’urar cirar kudi ta POS to wajibi ne a magance matsalar cikin awanni saba’in da biyu maimakon kwanaki biyar da ake yi a baya.
You must be logged in to post a comment Login