Labarai
CBN ya koka kan yadda ake wulakanta takardun Naira

Babban Bankin kasa, CBN, ya koka kan yadda wasu daga cikin mutane ke wulakanta takardun kudi na Naira, ya na mai cewa hakan na kara tsadar buga sababbi da maye gurbin wadanda suka lalace.
Mataimakin Gwamnan Bankin, Dakta Bala Bello, wanda Daraktan Sashen Kula da harkokin Kudi da Rassa, Dakta Adedeji Adetona ya wakilta, ya bayyana haka a Abuja, yayin kaddamar da wani gangami na wayar da kan al’umma kan kula da takardun kudin naira.
Dakta Bello ya ce naira ba kawai takardar bace, illa alamar martabar kasa da ikon Najeriya, da ya ce abubuwan da ake yi na sakaci kamar nadewa, yagawa, rubutu a kai, da yin watsi da su a lokutan bukukuwa na rage kimarta tare da kara tsadar kula da ita.
Ya yi gargadin cewa muddin ba a dauki matakan gyara ba, ‘yan kasa za su ci gaba da daukar nauyin kudin da ake buga sababbi domin maye gurbin wadanda aka lalata.
You must be logged in to post a comment Login