Labarai
CBN ya sanya hannun kan yarjejeniyar yin aiki da takwaransa na Angola

Babban bankin Najeriya CBN, ya sanya hannu kan takardar yarjejeniyar yin aiki tare da takwaransa na kasar Angola domin samar da ci gaba a tsakanin manyan bankunan Kasashen.
Kasashen dai sun kulla yarjejeniyar ne a Birnin Washington DC, yayin bikin shekara shekara da Bankin duniya da hadin gwiwar asusun bada lamuni na majalisar dinkin duniya.
Yayin taron shugaban baban bankin kasarnan Mohammed Abdullahi ya ce kulla yarjejeniyar, zai kawo ci gaba wajen shawo kan matsalolin da bankunan kasashen ke fuskanta, da kuma bunkasasu.
Mahimman fannonin da haɗin gwiwar za su shafa sun haɗar da sarrafa musanyar kudade, kasuwannin hada-hadar kuɗi, sarrafa asusun ajiyar kudaden waje, sarrafa kuɗin waje, da bincike da sanya ido.
You must be logged in to post a comment Login