Manyan Labarai
CBN zai fara aiwatar da shirin Cash less
Babban bankin kasa CBN yace za’a fara aiwatar da shirin Cash less a dukkanin kasar nan daga watan Maris din shekara ta 2020.
Babban bankin kasar ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da aka rarrabawa bankunan kasuwanci na kasar nan.
Haka zalika CBN din ya ce fara aiwatar da shirin zai nuna irin chanjin da ake yi akan sanya kudi acikin asusu ko kuma fitarwa.
Sanarwar ta ce za’a fara amfani da chanjin ne daga yau Laraba 18 ga watan Satumbar da Mike ciki Wanda za’a dinga chajin kashi 3 cikin 100 na kowane fitar da kudi da ya wuce dubu Dari biyar a rana guda.
A cewar babban bankin zai dinga chajin kashi 5 cikin 100 kan Asusun kasuwanci idan aka zari fiye da Naira miliyan 3.