Labaran Kano
CBN:kiwon Kaji na kawo gudunmuwar tattalin arziki
Babban bankin kasa (CBN), ya ce kiwon kaji shine harka da ya fi ba da gudunmawa ga tattalin arzikin kasar nan a bangaren noma da kiwo.
A cewar bankin na CBN hada-hadar noman kajin ya kai naira tiriliyan daya da Biliyan dari shida.
Gwamnan babban bankin na CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana haka yayin wani taro da ya gudanar da shugabannin jami’o’in kasar nan game da wani shirin farfado da noman kaji a Jami’oi.
Godwin Emefiele wanda mataimakin sa mai kula da harkokin tsare-tsaren tattalin arziki Okwu Nnanna ya wakilta, ya ce, noman kaji na ba da gudunmawar kaso ashirin da biyar ga gudunmawar da noma ke bai wa tattalin arzikin kasar nan.
Gwamnan na CBN ya kuma ce akwai kaji miliyan dari da sittin da biyar wadanda ke ba da gagarumin gudunmawa ga tattalin arzikin kasa.