Labaran Wasanni
Champion Leagues: Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Juventus

Zakarun gasar Champions Leagues ta shekarar 2020/2021 Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Juventus da ci 1-0 a wasan da suka fafata a ranar Laraba 29 ga Satumbar 2021.
Tunda fari dan wasan kasar Italiya da Juventus Fedirico Chiesa ne ya zura kwallon a minti na 46.
Nasarar da Juventus ta yi akan Chelsea ya bata damar darewa ta farko a rukuni na H da maki 6.
Yayin da ita kuma Chelseke take a mataki na biyu da maki uku a wasanni biyun da ta buga.
Wasan dai ya gudana a filin wasa na Allianz dake birnin Turin na kasar Italiya
You must be logged in to post a comment Login