Labaran Wasanni
Chelsea ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta Thomas Tuchel

Kungiyar kwallon kafa ta Chalsea dake ƙasar England ta sallami mai horar da ‘yan wasan ta Thomas Tuchel.
Hakan ya biyo bayan rashin nasara da kungiyar ta yi jiya Talata 6 ga watan Satumbar 2022 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Dinamo Zagreb da ci 1-0 a gasar cin kofin zakarun turai ta Champion League zagaye na farko.
A chalsea dai na fama da matsalolin rashin samun nasarar wasan ni tun da aka fara kakar wasanni ta bana a gasar Firimiya kasar Ingila.
Inda bayan buga wasanni 6 da fara gasar yanzu haka kungiyar ta chalsea na matsayin ta 6 kuma ta yi nasara a wasa 3 ta yi chanjaras a wasa 1 ta yi rashin nasara a wasa 2 kuma tana da maki 10.
You must be logged in to post a comment Login