Labarai
Cikakken tarihin sarkin musulmi Umaru Bin Ali – 1881
A rana irin ta yau ce a alif da dari takwas da tamanin da daya, aka nada Umaru Bin Ali a matsayin sarkin musulmi.
An haifi Sarkin Musulmi Umaru Bin Ali a alif da dari takwas da ashirin da hudu, ya kuma rike mukamin sarkin musulmi tsakanin shekarun alif da dari takwas da tamanin da daya zuwa ranar 25 ga watan Maris na alif da dari takwas da casa’in da daya.
Sarkin musulmin na tara tun jihadin Shehu Usmanu Danfodio ya gaji dan uwan mahaifinsa sarkin musulmi Mu’azu dan Muhammadu Bello ‘Da’ ga mujaddadi Shehu Usmanu Danfodio, wanda ya rasu a watan Satumban alif da dari takwas da tamanin da daya.
Haka zalika Umaru Bin Ali wanda mahaifinsa shi ne Aliyu Babba wato ‘Da’ ga Muhammadu Bello dan mujaddadi, a bangare guda kuma jika ne ga sarkin musulmi Muhammadu Bello sannan kuma tattaba kunnen mujaddadi Shehu Usmanu Dan fodio.
Kafin nadinsa a matsayin sarkin musulmi, umaru Bin Ali yana rike da sarautar sarkin Sudan, sannan yana zaune ne a Riba da ke garin Shinaka
A zamanin mulkinsa, ya ci gaba da dorawa kan ayyukan da sarkin Musulmi Mu’azu da Muhammadu Bello, suka fara, na yakar Sabon Birni da Madarunfa wanda yanzu gari ne da ke jamhuriyar Nijar da kuma Argungu biyo bayan karya yarjejeniyar zaman lafiya da Argungu ta yi.
Haka zalika kwamandan da ya jagoranci yakin shi ne sarkin Lifidi Lefau.
Bayanai sun tabbatar da cewa jan-daga da dakarun Kebbawa suka yi, ya sanya suka samu nasarar kan dakarun sarkin musulmi Umaru Bin Ali wanda a wannan gumurzu ne Sarkin Lifidi Lefau ya rasa ransa.
A shekarar alif da dari takwas da tamanin da biyar ne kuma Sarkin musulmi Umaru Bin Ali, ya sanya hannu kan yarjejeniya da turawan burtaniya ta hannun kamfanin Royal Niger.
A cewar jagoran kamfanin na Royal Niger Company, Mr Goldie, sarkin musulmi Umaru bin Ali ya amincewa kamfanin da ya gudanar da harkokin kasuwancinsa a yankin daular usmaniyya.
You must be logged in to post a comment Login