Labarai
CISLAC ta zargi DSS da kawo tsaiko kan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya
Kungiyar CISLAC mai sanya ido a kan ayyukan majalisun dokoki da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta zargi rundunar tsaro ta kasa DSS da kawo tsaiko a wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Shugaban kungiyar kuma wakilin kungiyar Transparency International mai yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan, Auwal Musa Rabsan Jani ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da Freedom Radio.
“Mun nemi shugaban DSS ya yi bincike kan yadda ma’aikatan sa suka shigo ofishin mu duk da ana cikin hutu suka kama bincike, ya kamata a san cewa dimukradiyya ta bada dama kowanne dan kasa ya fadi albarkacin bakin sa, irin wannan tamkar ana kokarin hana kungiyoyi su fito su yaki cin hanci da rashawa da wasu abubuwan da bai kamata ba a kasar nan”.
Rafsanjani ya kuma ce, “Tuni mun aike da takarda ga shugaban hukumar DSS da ya bincika a bi mana hakkin mu, domin duk abinda muke yi muna yin sa kan doka da oda don haka a bi mana hakkin mu”.
Auwal Musa Rabsan Jani, ya kuma kalubalanci jami’an tsaron DSS da firgita jami’an CISLAC yayin bukukuwan Kirsimeti, har ma ya ce lokaci yayi da ya kamata jami’an tsaro su rika bai wa al’umma damar fadar albarkacin bakin su ba tare da shigar da tsoro a zukatan su ba, don kawo karshen matsalolin da kasar ke fuskanta.
You must be logged in to post a comment Login