Labarai
Gwamnatin Kaduna ta dauki nauyin iyalan matashiyar da aka kashe a Marabar Jos

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya ce gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin kula da iyalan marigayiya Ummulkhairi Aliyu, wadda wasu fusatattun mutane suka kashe a yankin Maraban Jos da ke Ƙaramar Hukumar Igabi.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin za ta riƙa kula da mijin marigayiyar da kuma ‘ya’yanta huɗu, tare da ɗaukar nauyin karatunsu.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamaciyar a ranar Asabar, kusan makonni biyu bayan aukuwar lamarin.
An kashe marigayiyar Ummulkhairi Aliyu, malamar addinin Musulunci, a ranar 14 ga watan Yuni, bayan da wasu suka zarge ta da yunƙurin sace yara.
Rahotanni sun ce taron jama’a sun lakaɗa mata duka har ta mutu, sannan suka ƙona gawarta kafin jami’an tsaro su dawo da zaman lafiya a yankin.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Uba Sani ya yi Allah wadai da abin da ya faru, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin ɗabi’a.
Ya ce tun bayan da ya samu labarin kisan, ya umarci manyan jami’an gwamnati su kai ziyara ga iyalan domin jajanta musu, duk da cewa yana wajen jihar kan aikin hukuma.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati tana aiki tare da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa an gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a kisan gaban kotu.
A cewarsa, an gurfanar da mutum 41 kan zargin aikata kisan kai, yayin da aka kammala bincike kan wasu mutum 41, wanda ya kai jimillar mutane 82 da aka bincika.
Haka kuma, an gurfanar da mutum 30 bisa zargin haɗuwa ba bisa ƙa’ida ba.
Uba Sani ya ce babu wanda zai tsira daga hukunci idan aka same shi da hannu a wannan lamari, yana mai jaddada cewa babu wanda ke da ikon ɗaukar doka a hannunsa.
Ya kuma umarci a binciki rawar da wasu jami’an tsaro suka taka a lokacin da lamarin ya faru, musamman jami’in ‘yan sanda mai kula da yankin Maraban Jos.
Gwamnan ya ce duk wani jami’in tsaro da aka samu da sakaci ko rashin yin aikinsa yadda ya kamata zai fuskanci hukunci.
Kisan Ummulkhairi Aliyu ya jawo suka daga sassa daban-daban na ƙasar, inda shugabannin addinai, ƙungiyoyin fararen hula da masu rajin kare haƙƙin bil’adama suka buƙaci a tabbatar da adalci tare da ɗaukar matakan da za su hana irin wannan a nan gaba.
You must be logged in to post a comment Login