Coronavirus
Corona: An yiwa ƴan Najeriya sama da miliyan 3 rigakafi – Dakta Faisal
Hukumar kula da cibiyoyin lafiya a matakin farko ta ƙasa ta ce, sama da ƴan Najeriya miliyan uku ne suka karɓi cikakkiyar rigakafin cutar Corona.
Shugaban hukumar Dr Faisal Shuaib ne ya bayyana hakan a Abuja, a taron mako-mako da kwamitin shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar corona ke gudanarwa.
Ya ce, an yiwa sama da ƴan Najeriya rigakafin ne a tsawon watanni takwas da aka fara gudanar da rigakafin cutar.
Dakta Faisal Shu’aibu ya kuma ce, a ƙalla mutane 5, 891, 305 ne suka karɓi rigakafin kashin farko, adadin da ya nuna sun wakilci kaso 5.3 na yawan ƴan ƙasar.
Kazalika ya kuma ce wadanda suka karɓi rigakafin kashi na biyu sun kai dubu 3,252,067, adadin da ya nuna sun wakilci kaso 2.9 na yawan ƴan Najeriya.
Dakta Faisal Shu’aibu ya tabbatar da cewa, gwamnatin tarayya ta tanadi wadatacciyar rigakafin corona da zai isa a yiwa kaso mafi yawa na al’ummar ƙasar.
You must be logged in to post a comment Login