Labarai
Corona : Yau dalibai ke shiga mako na biyu da komawa makaranta a Kano
Yau Litinin ɗalibai a Kano ke shiga mako na biyu da komawa makaranta.
A ranar Litinin din makon da ya gabata ne aka buɗe makarantun firamare dana sakandire na gwamnati da kuma masu zaman kansu cikin tsauraran matakan kariya saboda cutar Corona a Kanon.
Kwamishinan ilimi na jihar Kano Malam Sanusi Sa’idu Ƙiru ya shaida wa Freedom Radio cewa kafin buɗe makarantun sai da aka yi feshin kashe ƙwayoyin cututtuka a makarantu, sannan an tanadi wuraren wanke hannu.
Kalubalen da muke fuskanta yawan dalibai don basu gurban karatu – Bello Dalhatu
Corona : Jihar Niger zata bude makarantu a mako mai zuwa
A nasu ɓangaren ɗaliban jihar Kano da suka koma karatu a makon da ya gabata sun bayyana farin cikinsu game da komawar, inda wasu ke cewa komawa makarantar ta rage musu zaman banza, wasu kuma na cewar sun manta inda aka kwana.
You must be logged in to post a comment Login