Labarai
Coronavirus: Shaguna sun fara daukar matakai a Kano
Rukunin shagunan sayar da kayayyaki na Ado Bayero Mall dake nan Kano ya dauki matakan tsaftace hannu ga masu shiga domin yin riga kafi ga cutar Coronavirus.
Sakamakon bullar cutar ta Coronavirus ta sanya mahukunta Ado Bayero Mall samar da wani sabon tsari da zai tilastawa dukkan me shiga rukunin shaguna wanke hannu da wani ruwa mai dauke da sinadarin kariya.
Wasu da muka iske a yayin da suke wanke hannuwan na su, sun bayyana mana cewa hakan tsari ne mai kyau, sai dai yana haifar da tsaiko kafin mutum ya samu shiga domin biyan bukatar sa akan lokaci.
Karin labarai:
Covid-19: Masana a Kano sun yi tsokaci kan Coronavirus
Covid19: Gwamnatin Kano ta samar da lambobin kira kan Coronavirus
Wakiliyar mu Zinnira Garba Baban Ladi ta rawaito mana cewa shugabar sashen kasuwanci ta Ado Bayero Mall din Hajiya Rabi Umar Tudunwada ta ce daukar wannan matakai ya zama tilas domin bayar da kariya ga abokan hurdar su.
Idan zaku iya tunawa dai bullar cutar Coronavirus a Najeriya ta sanya mahukunta na ta kokari wajen daukar matakan kariya game da cutar.
Ko a nan Kano ma, gwamnatin Kano ta dauki kwakwaran matakai ciki kuwa harda samar da lambobin tuntubar gaggawa ga duk wanda ya ci karo da alamomin wannan cuta.
You must be logged in to post a comment Login