Coronavirus
Coronavirus ta bulla a jihar Kogi
Hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC tace an samu bullar cutar Covid-19 a jihar Kogi.
Cikin jadawalin wadanda suka kamu da cutar da NCDC ta fitar a ranar Laraba tace an samu mutane 2 dake dauke da cutar ta Coronavirus a jihar Kogi.
Kafin wannan rana dai jihar Kogi na cikin jihohi biyu a Najeriya da ba a samu bullar cutar ta Covid-19 ba, yanzu haka dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a Najeriya.
A alkaluman da NCDC ta fitar a daren Laraba ta ce yazuwa yanzu mutane 8,733 ne suka kamu da cutar Covid-19 a sassa daban-daban na kasar nan.
Kuma 2,501 sun warke sarai har an sallame su.
Sai mutane 254 da cutar ta hallaka a Najeriya.
Hukumomi dai a kasarnan na cigaba da daukar matakan dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.
A ranar Laraba ne gwamnatin tarayya ta amince ayi amfani da magungunan gargajiya wajen yaki da cutar ta Covid-19 a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login