Labarai
COVID 19 : An bakado cibiyoyin bogi na gwajin Corona a Lagos
Gwamnatin jihar Lagos, ta bankado tare da gargadin al’ummar jihar kan sababbin cibiyoyin bogi na gwajin cutar Corona da wasu ‘yan damfara suka bude a jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar Akin Abayomi ne, ya bayyana haka a yammacin jiya Litinin ya yin tattaunawar sa da ‘yan jaridu akan sabbabbin cibiyoyin gwaji guda 10 da jihar ta bude a kananan hukumomin 10, da ake da yawaitar masu cutar.
Kwamishinan ya kara dacewa, gwamnatin jihar ba zata lamunci aikin wasu bata gari ba dake kokarin mai da hannun Agogo baya, za kuma ta soke fasfo din duk wasu matafiya da basu yarda a yi musu gwajin cutar ba.
Abayomi, yace zuwa yanzu gwamnatin jihar ta kara yawan adadin gwajin da ake yiwa al’umma a rana daya daga 2,000 zuwa 3,000, domin samun saukaka lamarin da yiwuwar sawo kan cutar ko dakile ta gaba daya
You must be logged in to post a comment Login