Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Alhassan Rurum ya yiwa Buhari ta’aziyyar rashin Abba Kyari

Published

on

Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure, kuma shugaban ‘yan majalisar wakilai na kasa shiyyar Arewa maso yamma Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya aike da sakon ta’aziyyar sa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Malam Abba Kyari.

Yayin wata ganawa da wakiliyar mu Umma Sulaiman Sagagi, Rurum ya bayyana rashin marigayi Abba Kyari a matsayin babban rashi ga al’ummar kasarnan.

Har ila yau, Alhassan Rurum yayi addu’ar Allah ya gafartawa marigayin ya sanya aljannah makoma, da kuma fatan Allah ya sanyawa bayansa albarka.

A wani bangaren kuma Alhaji Kabiru Alhassan Rurum yayi amfani da wannan dama domin mika sakon ta’aziyyar sa ga Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Tafida Abubakar Ila da masarautar Rano bisa rashin dan uwa ga sarkin Alhaji Ali Ma’aji Rano, wanda ya rasu bayan ya sha fama da jinya.

Rurum ya ce marigayi Alhaji Ali Ma’aji mutum ne da ya taimakawa al’umma a lokacin da yake raye, sannan yayi add’ar Allah ya jikansa ya kuma sanya aljannah ta zamo makoma a gareshi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!