Labarai
COVID-19: An fara feshin magani kan Corona a masana’antun dake Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata ci gaba da bibiyar masana’antun dake jihar Kano don tabbatar da sun bi shawarwari da dokokin da masana kiwon lafiya suka sanya domin dakile cutar Corona.
Kwamishinan muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso, shi ne ya bayyana hakan a yau Lahadi, yayin da ma’aikatar ke gudanar da feshin maganin a wasu masana’antun jihar.
Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce, za a dauki matakin hukunci ga duk masana’antar da aka samu da bijirewa bin ka’idojin kiyaye lafiyar ma’aikatan ta.
Hotuna ayayin feshin maganin
Da yake jawabin godiya da tallafin feshin maganin da aka yiwa masana’antar sa, shugaban rukunin masana’antun sarrafa fata da buhu dake Chalawa Fadul Kattar ya ce za su ci gaba da biyayya ga umarnin gwamnati tare da tabbatar da an farfado da tattalin arzikin jihar Kano.
Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa an gudanar da feshin maganin a masana’antun Chalawa da Sharada inda aka same su da bin dokokin da suka alkawarta.
You must be logged in to post a comment Login