Connect with us

Addini

Ganduje zai dauki alarammomi 60 domin koyar da almajirai a Kano

Published

on

Hukumar kula da tsangayun Islamiyya ta Jihar Kano ta ce, za ta dauki alarammomi sittin domin ci gaba da koyar da almajiran da aka dawo mata da su daga wasu jihohin Kasar nan.

Shugaban hukumar Gwani Yahuza Gwani Dan-Zarga ne bayyana haka yau, a lokacin da take tantance alarammomin a shalkwatar hukumar da ke nan Kano.

Shehin Malamin ya kuma ce, gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa hukumar umarnin baiwa almajiran ilimin addini da na zamani yadda ya kamata.

Gwani Yahuza Gwani Dan-Zarga ya kuma ce, makarantu goma-sha shida ne za a tura alarammomi domin karantar da almajiran karatun boko da na zamani.

Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa, alarammonin da za a dauka don koyarda da daliban sun fito ne daga kananan hukumomin Jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!