Connect with us

Coronavirus

Covid-19: An saka “Lock Down” a kananan hukumomi 3 na jihar Bauchi

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanya dokar kulle da zaman gida ta tsawon kwana goma a kananan hukumomin Katagum, da Giade da karamar hukumar Zaki domin dakile yaduwar cutar Covid-19.

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi inda yace dokar zata fara aiki daga karfe 6 na yammacin ranar Talata.

Sanata Bala Muhammad yace, an dauki wannan mataki ne ganin yadda ake samun rahotonnin yaduwar cutar a yankin wadannan kananan hukumomi.

Kazalika gwamnan yace tuni kwamitin yakar Corona na jihar sun baza komarsu domin daukar dukkan matakan da ya dace wajen dakile cutar a yankunan.

A karshe gwamna ya bada umarni ga kwamitin rabon kayan tallafin Corona na jihar karkashin sarkin Bauchi Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu da su kai agajin gaggawa ga al’umma a yankunan da dokar kullen zata fara aiki.

Karin labarai:

Da dumi-dumi Gwamnan jihar Bauchi ya kamu da COVID-19

COVID 19: Gwamnan jihar Bauchi ya killace kansa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,220 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!