Connect with us

Labarai

Yawan masu dauke da cutar HIV a Bauchi ya sauka – Gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce adadin masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki a jihar ya sauka daga kaso 6, da ake dasu a tun daga shekarar 2001 zuwa sifili da digo 4 a shekarar 2019.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr Aliyu Maigoro ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi ga me da matsayar jihar kan masu dauke da cutar, a wani bangare na bikin ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki da aka gudanar a jiya.

Maigoro ya ce, a yanzu haka mutane dubu ashirin da biyar da dari takwas da tara ne ke rayuwa da cutar a kananan hukumomi 20 na jihar  Bauchi, cikin su kuwa mutum dubu ashirin da dari tara da sittin da daya suna samun kulawa daga cibiyoyin lafiya.

Cikin jawabin nasa, ya ce jihar za ta tabbatar da kowanne ma’aurata sun gudanar da gwaji kafin uare don dakile yaduwar cutar a tsakanin al’umma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!