Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

COVID 19: Gwamnan jihar Bauchi ya killace kansa

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa Gwamnan jihar Sanata Bala Muhammad ya killace kansa biyo bayan musabiha da ya yi da dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a filin jirgin sama na jihar Legas.

Bayanin Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai dauke da sa hannun babban mataimaki ga gwamnan kan yada labarai Mukhtar M Gidado.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar dakile cutuka ta kasa NCDC ta tabbar da cewa dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa na dauke da cutar.

Sanarwar ta ce kawo yanzu gwamnan bai nuna wata alama ta rashin lafiya ba, sai dai gwamnan ya killace kansa sakamakon shawara da ya samu daga hukumar dakile cutuka ta kasa NCDC, inda ta bukaci ya killace kansa domin gudun kamuwa daga cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!