Coronavirus
Covid-19: An sanya ranar komawa makarantu a Nijar
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa a matsayin ranar da za’a sake bude makarantun bokon kasar bayan matakin rufe su na tsawon lokaci sakamakon bullar cutar Covid-19 a kasar.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin ministan ilimi mai zurfi na kasar Malan Yahuza Sadisu Madobi a yayin wani taron manema labarai da ya kira a babban birnin Yamai.
Ministan ya ce za a sake bude makarantun ne cikin matakan rigakafin cutar Coronavirus a cikin makarantun domin kammala shekarar karantun ta bana da ministan ya ce an ci sama da kashi 50 cikin 100 na karatun.
Labarai masu alaka:
Buhari zai yi titi daga Sokoto zuwa Nijar
Gwamnatin kasar Jamhuriyar Nijar ta ce zata yi aiki da kasarnan don bunkasa ilimi
Wakilin mu Yakuba Umaru Maigizawa ya waito mana cewa ministan ya kara da bayyana ranakun da za’a koma karatun na shekarar kamawa.
Sai dai bai bayyana ba ranar da za’a gudanar da jarabawar karshen karantun shekarar ta bana amma ya ce nan gaba gwamnatin za ta bayyana ranakun.
You must be logged in to post a comment Login