Coronavirus
Covid-19: Babu hawan sallah a Kano
Maimartaba Sarkin Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al’ummar Kano da su kiyaye dangane da yanayin da ake ciki na annobar Covid-19 da ta janyo sauyawar al’adun fada.
Sarkin ya bayyana hakanne a daren Asabar a Kofar Kwaru yayin da yake jawabi a gaban manyan hakiman sa kan yadda za a gudanar da sallar bana.
Maimartaba Aminu Ado ya ce babu hawan sallah na al’ada da masarautar Kano ta sabayi duk shekara saboda yanayin Corona.
Sarkin ya kara da cewa maimakon hakan Sarki zai tafi idi a kafa, inda zai fito ta kofar Fatalwa har zuwa filin idi na Kofar Mata da safe.
Bayan an idar da sallar idi kuma Sarkin zai biyo ta unguwar Kofar Wambai da Zage, sannan ya biyo ta Dorayi da Shahuci daga nan ya zarto zuwa Kofar Kwaru a Mota.
Ana sa ran Sarkin zai yi jawabi ga al’ummar Kano bayan sakkowa daga sallar idin a Kofar Kwarun kamar yadda al’adar masarautar Kano take.
Wakilinmu na fadar sarkin Kano Muhammad Harisu Kofar Nassarawa ya rawaito mana cewa Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jajantawa al’ummar Kano sakamakon rashe-rashen da aka samu sannan yayi fatan marasa lafiya Allah ya basu lafiya.
A karshe Sarkin yayi kira ga al’ummar Kano da su cigaba da kiyayewa tare da yin biyayya ga matakan da masana kiwon lafiya suka sanya wajen dakile yaduwar cutar Corona.
A shekarun baya dai, kafin annobar Covid-19 ta bullo akan shafe kwanaki biyar ana gudanar da hidimomin al’ada na masarautar Kano a yayin bikin karamar sallah.
You must be logged in to post a comment Login