Coronavirus
Covid-19: Buhari ya tsawaita dokar kulle a Kano
Kwamitin karta-kwana kan annobar Covid-19 na kasa ya sanar da karin sati biyu kan dokar kulle da zaman gida a jihar Kano.
Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha shi ne ya sanar da hakan a yayin da yake jawabin taron bada bayani da kwamitin karta-kwana keyi.
A wani bangaren kuma, yanzu haka gwamnan Kano ya shiga zaman ganawar sirri da malaman addini na jihar.
Mutane a Kano na dakon sanarwar da za a fitar bayan kammala wannan zaman.
You must be logged in to post a comment Login