Coronavirus
Covid-19: Dokar kulle ta taimaka wajen dakile cutar – Kwamishinan Lafiya
Ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano, ta bayyana cewar dokar kulle da aka saka sakamakon cutar corana ta taimaka wajen dakile yaduwar.
Kwamishinan Lafiya Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan tashar Freedom Radio.
Ya ce, duba da yadda Kano take da yawan al’ummah yanzu haka ana korarin bincike kan cutar don ganin an dakile ta a jihar baki daya.
Ana ci gaba da duba marasa lafiya ta wayar hannu a Kano
Ma’aikatan lafiya 14 sun kamu da Corona a Katsina
A nasa bangaren Dakta Tijjani Hussain na kwamatin karta-kwana kan dakile yaduwar cutar ta corona, da shima ya kasance a cikin shirin cewa yai kwamatin na korarin wayar da kan al’umma game da cutar duba da cewar har yanzu akwai wanda basu yadda da cutar ba.
Bakin sun shawarci al’umma da su kasance masu kula da tsaftar muhallin su tare da wanke hannu da kuma kaucewa cakuduwar cikin jama’a domin kare lafiyar su.
You must be logged in to post a comment Login