Coronavirus
Covid-19: El-rufa’i ya kara tsawaita dokar kulle a Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-rufai ya kara tsawaita dokar kulle da zaman gida tsawon makonni biyu a jihar.
Mataimakiyar gwamnan jihar Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta bayyana hakan, cikin wata sanarwa da fitar a yammacin Talatar nan wanda ta ce gwamnati ta tsawaita dokar kulle da zaman gida a jihar ne domin dakile cutar Corona.
Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar ta Kaduna da su cigaba da daukar matakan kariya da masana kiwon lafiya suka gindaya na sanya takunkumin rufe baki da hanci, da yawaita wanke hannu da kuma bada tazara a tsakanin juna, sannan al’umma su kaucewa taron jama’a masu yawa.
Haka kuma gwamnatin jihar ta ce a yanzu al’umma za su rika sararawa a ranaku guda uku a jere cikin mako ranakun sune, ranar Talata Laraba da kuma ranar Alhamis.
Kananan wuraren kasuwanci da aka amince su bude za su rika fitowa a wadannnan ranaku daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma.
Su kuwa jama’a masu zirga-zirga za su rika fita ne daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a ranakun.
Har ila yau gwamnatin Kaduna ta gargadi ‘yan kasuwannin da ba a amince musu su bude ba, kan suyi biyayya da dokokin da aka sanya.
Har ila yau, sanarwar ta kara da cewa kotun tafi da gidanka zata cigaba da ayyukanta domin hukunta masu karya dokoki da kuma masu yawon dare a yayin dokar kullen.
Haka kuma gwamnatin Kaduna tace makarantu da wuraren ibadu dukkansu za su cigaba da zama a kulle.
Sanarwar tace yanzu haka jihar Kaduna ta yiwa mutane dubu daya da dari tara (1900) gwajin cutar Corona inda ta samu mutane 189 dake dauke da cutar.
A karshe gwamnatin Kaduna ta ce cikin wannan karin makonni biyu zata mayar da hankali wajen kara habaka ayyukanta na yaki da cutar Coronavirus.
*BS*
You must be logged in to post a comment Login