Labarai
Covid-19: Ganduje ya karawa ma’aikata hutun sati 2
Gwamnatin jihar Kano ta karawa ma’aikatan jihar hutun sati 2 a wani bangare na ci gaba da tsaurara matakan hana annobar Covid-19 shigowa jihar Kano.
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano Abba Anwar ya aikowa Freedom Radiyo a yammacin yau litinin.
Sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar rahoton kwamitin gwamnatin jihar Kano na tattara tallafin cutar Corona wanda shugaban kwamitin Farfesa Yahuza Bello ya mika masa a fadar gwamnatin jihar Kano.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin wa’adin hutun sati 2 na farko da gwamnatin ta bayar ya kare a yau litinin, inda sanarwar ta ce karin hutun zai fara daga gobe talata 7 ga watan Aprilu.
You must be logged in to post a comment Login