Labarai
Covid-19: Gwamnatin jihar Jigawa ta samar da gadaje sama da 300
Gwamnatin jihar jigawa ta ce ta samar da cibiyoyi guda uku da za su dauki gadaje sama da 300 a shirin karta kwana da take yi wajen yaki da cutar Covid-19.
Kwamishinan Lafiya kuma shugaban Kwamitin karta kwana na yaki da cutar Covid-19 a jihar ta Jigawa Dakta Abba Zakari Umar ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da manema labarai game da matakan da gwamnati ke dauka na yaki da cutar Covid-19.
Abba Zakari Umar ya ce za su ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin lafiya na nan Kano don ganin cutar bata shigo jihohin ba.
Jihar Jigawa ta yi wa Kano fintinkau a taimakawa marasa karfi
Covid-19: Za a rufe makarantu a jihohin Arewa masu yamma
Dakta Abba Zakari Umar yace adon haka ne a jiya gwamnan jihar ta Jigawa Badaru Abubakar ya kara wa’adin makwanni biyu ga ma’aikatan jihar tare da kuma aiki kafada da kafada da malamai wajen wayar da kan mutane game da cutar.
Da yake jawabi yayin taron shugaban gudanarwa na kwamitin kartakwana na yaki da cutar Covid-19 a karamar hukumar Gwaram a jihar Alhaji Muhammad Muhammad Sara, ya ce a jiya ba’a gudanar da cin kasuwa ba a kasuwar Sara dake Gwaram wanda ke diban dubban mutane a wani yunkuri na hana cakuduwar jama’a.
You must be logged in to post a comment Login