Labarai
Covid-19: Gwamnatin tarayya ta mai da martani kan kin amincewa da wasu ‘yan majalisa sukai kan tantance su
Fadar shugaban kasa ta mai da martani game da yadda wasu daga cikin ‘yan majalisun wakilan kasar nan suka ki amincewa ayi musu gwajin cutar Corona Virus a filayan jirgin saman kasar nan lokacin da suka dawo tafiye-tafiyen su.
Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari da ya aikewa da shugaban majalisar wakilai Mr Femi Gbajabiamila.
Sanarwar ta kuma ce hakan ne ya sanya ma’aikatar lafiyar ta kasa ta ja hankalin gwamntain tarayya kan wannan al’amari, kasacewar hakan wasa ne da lafiyar al’ummar Najeriya.
Takardar da fadar shugaban kasar ta aikewa da shugaban majalisar ta wakilai Femi Gbajabiamila mai dauke da kwanan watan Ashirin da daya ga watan da muke ciki na Maris ta ce ya zama wajibi ga kowanne dan kasar nan da zai shigo daga wata kasar ya amince a yi masa gwajin cutar ta Corona kafin shigowa sa kasar nan.
Haka kuma sanarwar ta bukaci shugaban majalisar ta wakilai ya umarci dukkan yan majalisar da suka ki amincewa a yi musu gwajin su ziyarci hukumar takaita yaduwar cututtuka ta NCDC dan gwada lafiyar su.
You must be logged in to post a comment Login