Coronavirus
Covid-19: Kaso 42 na ma’aikatan kasar nan sun rasa ayyukan su- NBS
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta ce, cutar corona ta yi sanadiyar mayar da kaso arba’in da biyu na ma’aikatan kasar nan marasa aikin yi.
Hukumar ta NBS ta wallafa hakan ne ta cikin wani rahoton da ta fitar kan halin da tattalin arzikin kasar nan ya shiga sakamakon cutar ta covid-19.
A cewar NBS, mawuyacin hali da tattalin arzikin kasar nan ya shiga sanadiyar dokar kulle ya yi illa fiye da na shekarun dubu biyu da sha bakwai da dubu biyu da goma sha takwas.
An samu raguwar masu cutar Corona a ranar Alhamis
NAHCON: Muna jiran matakin Saudiyya game da aikin Hajjin bana
Rahoton hukumar ta NBS ya kara da cewa, dokar kullen ta shafi kowane bangare na tattalin arziki wanda a dalilin haka jama’a da dama suka rasa ayyukansu.
You must be logged in to post a comment Login