Labarai
Covid-19: Kungiyar Youths Helping Hands ta bada tallafi a Kiru
Wata Kungiyar ci gaban matasa mai suna Youth Helping Hands ta gudanar da bikin wayar da kan al’umma kan yadda zasu kare kansu daga annobar Corona Virus a karamar hukumar Kiru dake jihar Kano
Haka kuma a yayin taron kungiyar ta bayar da tallafin sinadarin wanke hannu wato Hand Sanitizers ga al’ummar yankunan karamar hukumar tare da nuna musu yadda zasu yi amfani da shi.
Da yake jawabi a yayin bayar da tallafin, Shugaban kungiyar Jibril Nasir Mu’azu Kiru yace ganin yadda annobar ke ci gaba da yaduwa, akwai bukatar wayar da kai tare da tallafawa al’umma musamman ma na karkara.
Ya ce dama sun kafa kungiyar ta Youths Helping Hands ne nufin taimakawa mutane marasa karfi tare da wayar musu da kai kan al’amuran rayuwar yau da kullum.
Ya kara da cewa a irin wannan lokaci da ake ciki na annobar Corona Virus, al’ummar karkara suna bukatar agaji tare da tare da wayar da kai kan yadda zasu gane wannan cuta tare da yadda zasu kiyaye yaduwarta.
Da yake magana a madadin al’ummar da suka amfana da tallafin Hakimin Kiru Alhaji Garba Alhaji ya godewa kungiyar ta Youth Helping Hands bisa zabar karamar hukumar domin bayar da wannan tallafin inda ya bukaci al’umma dasu rinka bin ka’idojin da hukumomin lafiya suka bayar na hana yaduwar wannan cuta.
A karshe, Ma’ajin kungiyar Umar Mustapha Kiru ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da tallafawa al’umma musamman ma a wannan lokaci a ake fama da annobar Covid 19, inda ya bukaci sauran kungiyoyin matasa da su rungumi dabi’ar tallafawa mabukata.
You must be logged in to post a comment Login