Kiwon Lafiya
COVID-19: Mun bankado matsalolin da bangaren kiwon lafiya ke fuskanta a Afrika – WAHO
Kungiyar lafiya ta kasashen yammacin Afrika WAHO ta ce ta gano yadda cutar COVID-19 ta bankado matasalolin da bangaren kiwon lafiya ke da shi a asibitocin kasashen Afrika ta yamma.
Da yake ganawa da manema labarai kan bikin cikar kungiyar shekaru 33 da kafuwa ta kafar Internet da kasashen Afrika goma sha biyar, shugaban kungiyar Farfesa Stanley Okolo ya ce gwamnatoci ba sa maida hankali wajen mangance matsalolin da al’umma ke fuskanta a asibitocin nahiyar Afrika.
Farfesa Stanley Okolo ya Ambato wasu daga cikin matsalolin da suka hada, rashin kayayyakin aiki da likitoci da dakunan gwaje-gwaje da magun-guna da na’urar gwada zafin jiki da kuma rashin alluran riga kafi.
Shugaban ya kara da cewar annobar Korona ta sanya an gano matasaloli masu tarin yawa da kuma hanyoyin da za’a bi wajen shawo kan su.
You must be logged in to post a comment Login