Connect with us

Kiwon Lafiya

COVID-19: Mun bankado matsalolin da bangaren kiwon lafiya ke fuskanta a Afrika – WAHO

Published

on

Kungiyar lafiya ta kasashen yammacin Afrika WAHO ta ce ta gano yadda cutar COVID-19 ta bankado matasalolin da bangaren kiwon lafiya ke da shi a asibitocin kasashen Afrika ta yamma.

Da yake ganawa da manema labarai  kan bikin cikar kungiyar shekaru 33 da kafuwa ta kafar Internet da kasashen Afrika goma sha biyar, shugaban kungiyar Farfesa Stanley Okolo ya ce gwamnatoci ba sa maida hankali wajen mangance matsalolin da al’umma ke fuskanta a asibitocin nahiyar Afrika.

Farfesa Stanley Okolo ya Ambato wasu daga cikin matsalolin da suka hada, rashin kayayyakin aiki da likitoci da dakunan gwaje-gwaje da magun-guna da na’urar gwada zafin jiki da kuma rashin alluran riga kafi.

Shugaban ya kara da cewar annobar Korona ta sanya an gano matasaloli masu tarin yawa da kuma hanyoyin da za’a bi wajen shawo kan su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!