Connect with us

Coronavirus

Covid-19: Mutum na 3 ya rasu sanadiyyar Corona a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa tace mutum na 3 ya rasu sakamakon cutar Covid-19 a jihar.

Kwaminshinan lafiya kuma shugaban kwamatin dakile yaduwar cutar a jhar jigawa Dakta Abba Umar ne ya bayyana hakan ga manema Labarai.

Kwaminshinan ya kara da cewa mutumin daya rasu dan jihar Kano ne a cibiyar killace masu dauke da cutar dake Dutse.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito kwaminshinan na cewa mutum 2 cikin 3 da suka rasu maza ne wadda na farko ya fito ne daga karamar hukumar Dutse sai mace guda yar karamar hukumar Miga da kuma na yanzu dan asalin jihar Kano.

Ya zuwa yanzu dai mutane 169 suka kamu da cutar a Jigawa yayin da 7 daga ciki sun warke sumul amma sallamesu.

Karin Labarai:

Za a gina cibiyar gwajin Corona a Jigawa

Almajirai 40 da Kano ta mayarwa da Jigawa na dauke da cutar Corona

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!