Labarai
Covid-19: Najeriya za ta iya samun durkushewar tattalin arziki
Shararren Malami akan zamantakewar al’umma na jamiar Bayero ta Kano Farfesa Sani Lawan ya ce annobar corona za ta haifar da matsalar durkushewar tattalin arzikin kasar nan da ma wasu kasashen sakamakon dukkanin wasu hada hada da ake gudanarwa sun tsaya sanadiyyar wannan cutar.
Farfesa sani lawan manumfashi ne ya bayyana hakan jim kadan bayana kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radiyo da ya gudana da safiyar yau laraba wanda ya mai da hankali wajan tattaunawa kan hanyoyin da ya kamata al’ummah su dauka dan ganin an kare kai daga wannan cutar.
Sani Lawan Manumfashi ya kara da cewar wannan matakin da gwamnati ta dauka na takaita cakuduwa a tsakanin al’umma, dan kare kai daga wannan cutar,amma yana da kyau gwamnatin ta yi wani abu wajan ganin an fito da wani tsarin da talaka zai samu wani abu duba da cewar wannan mataki zai shafi rayuwar sa ta yau da kullum.
Farfesan ya kuma kara da cewar ya kamata hukumomi su sanya idanu akan mutane masu sana’ar jari bola duba da cewar bola na tattare da dukkanin wasu kwayoyin cututuka da ke yaduwa a tsakanin al’umma.
Sani Lawan Manumfashi ya kuma bukace gwamnati da ta kasance tana shirya wasu shirye-shirye dan kara wayar da kan al’umma game da wannan cutar dan kai daga fuskantar barazanar cutar a jihar nan.
You must be logged in to post a comment Login