Labarai
Labari mai dadi: Ranar Lahadi ba a samu bullar Corona ba a Kano
Kididdigar cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta nuna cewa a ranar Lahadin nan ba a samu bullar cutar Coronavirus a jihar Kano ba.
Alkaluman hukumar ta daren Lahadi ta ce an samu karin mutane 86 da suka kamu da cutar a ranar Lahadin.
Jihar Legas ce ta farko wadda ta samu karin mutane 70 sai birnin tarayya Abuja da ya samu karin mutane 7, yayin da jihar Katsina ta samu karin mutane 3, Jigawa ta samu karin mutum 1, jihar Bauchi ma karin mutum 1 sai jihar Borno da ta samu mutum daya.
NCDC ta kara da cewa akwai mai dauke da cutar guda daya dan asalin jihar Jigawa wanda aka mayar dashi zuwa Jigawan daga Kano saboda haka Izuwa yanzu Kano tana da mutane 36 da suka kamu da cutar.
Alkaluman ranar Lahadin yace a yanzu Najeriya tana da mutane 627 da suka kamu da cutar, 170 daga ciki sun warke, yayin da 21 suka mutu.
You must be logged in to post a comment Login