Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An samu karin mutum 6 masu dauke da Coronavirus a Kano

Published

on

Hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce an samu karin mutane 6 da sakamakon gwajin da aka yi musu ya nuna cewa suna dauke da cutar Coronavirus a Kano.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook da misalin karfe 10:10 na daren jumu’a ta ce yanzu haka Kano tana da mutane 27 masu dauke da cutar.

Hukumar ta ce a yau an samu karin mutane 51 da suka kamu da cutar a Najeriya.

Mutane 32 a jihar Legas, mutum 6 a Kano sai mutum 5 a jihar Kwara yayin da Abuja ta samu karin mutum 2 jihar Oyo ma ta samu mutum 2 a jihar Katsina ma an samu mutum 2.

Yayin da jihojin Ogun da Ekiti suka samu mutum dai-dai.

Zuwa alkaluman yau jumu’a adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun kai 493 a sanarwar ta NCDC.

Mutane 159 daga ciki sun warke, mutum 17 kuma sun rasa ransu sanadiyyar cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!