Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Yanzu-yanzu: An samu karin mutum 10 sun kamu da Coronavirus a Kano

Published

on

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce an samu karin mutum 10 da suka kamu da kwayar cutar Coronavirus yau Asabar a Kano.

Cikin sabbin alkaluman kididdigar cutar da NCDC ta wallafa a shafinta na Facebook da misalin karfe 10:40 na dare tace yanzu jihar Kano tana da mutane 37 wadanda suka kamu da cutar.

Sanarwar ta kara da cewa an samu karin mutane 49 da suka kamu da cutar a yau Asabar a fadin Najeriya.

A kididdigar ta daren Alhamjs jihar Legas ce ke kan gaba wadda ta samu karin mutane 23 sai birnin tarayya Abuja da ya samu karin mutane 12.
Jihar Kano ce ke kan mataki na uku inda ta samu karin mutane 10, jihar Ogun ta samu karin mutum 2, yayin da jihohin Oyo da Ekiti suka samu karin mutum dai-dai.

A kididdigar ta yau NCDC ta ce Najerjya tana da mutane 542 da suka kamu da cutar Coronavirus, inda 166 daga ciki suka warke, mutane 19 daga ciki kuma suka rasu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!