Labaran Wasanni
COVID-19: Senegal na shirin ficewa daga wasan karshe na share fagen shiga gasar Olympic
Kasar Senegal za ta fice ba tare da shiri ba daga wasannin kwallon kwando na share fagen shiga gasar Olympic sakamakon barkewar cutar Corona a kasar.
Hukumar kwallon Kwando ta duniya FIBA ce ta tabbatar da tilastawa kasar ficewa daga wasannin duba da yadda annobar Corona take kara kamari a kasar.
Rahotanni na cewa, ‘yan wasa uku da kuma wani mamba a tawagar ‘yan wasan kasar ta Senegal sun kamu da cutar COVID-19.
Haka ne ya tabbatar da cewa kasar ba za ta samu damar zuwa kasar Serbia ba domin fafata wasannin karshe da za a fara ranar Laraba 30 ga watan Yunin 2021.
You must be logged in to post a comment Login