Labarai
COVID- 19 ‘Yan Najeriya mazauna kasashen ketare 288 ne suka dawo gida

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta sanar da cewa ‘yan Najeriya 288 ne suka dawo daga Hadaddiyar Daular Larabawa inda suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja yau.
Adadin da ya kawo mutane 2,641 kenan da aka kwaso daga Hadaddiyar Daular Larabawa tun bayan barkewar annobar cutar Covid-19.
Hukumar ta wallafa wannan sakon ne a shafinta na tiwita yau, inda ta ce za a yi wa mutanen gwajin kwayar cutar Corona, sannan kuma za a killace su har na tsawon makonni biyu kafin barinsu su tafi garuruwansu.
You must be logged in to post a comment Login