Coronavirus
Covid-19: Za a cigaba da sallah cikin jam’i a Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta amince a rika gudanar da sallar jam’i, a garuruwan da dokar kulle ta shafa na kananan hukumomin jahar guda 8 da cutar ta bulla.
Gwamnan jihar Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ne ya sanar da haka ga manema Labarai da yammacin talatar nan a fadar mulkin Gwamnatin jihar ta Jigawa.
Haka kuma badaru yace gwamnatin ta amince da hakanne, domin al’umma su gudanar da ibada, da kuma taya gwamnati addu’ar fita daga wannan yanayi na cutar COVID-19.
Karin labarai:
Za a gina cibiyar gwajin Corona a Jigawa
Almajirai 40 da Kano ta mayarwa da Jigawa na dauke da cutar Corona
To sai dai gwamnan yace duk da an amince a cigaba da gudanar da sallar juma’ar ya zama dole al’umma su rika dabbaka tsarin bada tazara tsakanin juna da kuma sanya abin rufe baki da hanci da dai sauran mataki.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito gwamnan na cewa burin gwamnatin Jigawa kawo karshen cutar gaba daya.
You must be logged in to post a comment Login