Labaran Wasanni
Covid- 19: Zamu dawo gasar Serie A Gabrielle Gravina
Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Italiya, (FIGC)Gabriele Gravina, yace zasu dawo karasa gasar kakar wasan bana na shekarar 2019/20.
An dai dakatar da gasar ta kasar Italiya, a watan jiya, sakamakon bullar cutar Corona, wanda hukumar tace ba za’a dawo gasar ba har sai an tabbatar da kawar da cutar.
Gwamnatin kasar Italiya a baya, ta kara wa’adin killace al’umma da zirga zirga, zuwa ranar 03 ga watan Mayu, sai dai rahotanni daga kasar ta Italiya, sun tabbatar dacewar kungiyoyin gasar sun bukaci dawowa a cikin wannan watan don kammala gasar kakar bana, a cikin watan Yuli.
Wasu kungiyoyin basa goyon bayan dawowa cigaba da gasar, sai dai kuma Gravina yace akwai yunkurin dawo wa akan lokaci do cigaba da gudanar da gasar.
Labarai masu alaka.
Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni
An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona
Fatan mu shi ne fara gasar da wuri,inji Gravina don kammala ta kan lokaci kasancewar rashin yin hakan zai kawo koma baya kwarai da gaske
Zuwa yanzu haka cutar ta Coronavirus ta kashe mutum 114,170 a fadin duniya cikin mutum 1,851,400 da suka kamu da cutar.
Daga kasar ta Italiya an samu mutuwar mutum 19,890 a cikin mutane 156,360 da suka kamu da cutar.
You must be logged in to post a comment Login