Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Covid -19: Abi doka da shawarar ma’aikatan lafiya-Sarkin Zazzau

Published

on

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya yi kira ga al’ummar kasar Zazzau da jihar Kaduna gaba daya da su zama masu bin doka da oda, da karbar shawarwarin masana harkokin lafiya don kaucewa kamuwa da yaduwar Annobar Corona Virus.

Mai martaba Sarkin , ya yi kiran ne a yayin wata ganawa da ‘yan  jaridu da kuma kira ga al’umma daya gudana a fadar sa yau dangane da halin da ake ciki na cutar mai lakabin Covid 19.

Alhaji Shehu Idris, yace yin hakan ya zama wajibi duba da yadda cutar ke kara yaduwa, wanda hakan ya sa tilas hukumomi da masu ruwa da tsaki su dauki matakan da suka kamata don ganin an gudu tare da tsira- tare.

Labarai masu alaka.

Covid-19: Maryam Abacha ta tallafawa mabukata da kayan abinci

Kyautatawa mabukata zai taimaka wajen ragi radadi- Sarkin Alkalman Kano

Sarkin ya kuma umarci al’umma dasu kai rahoton wanda suka ga yana  da alamun cutar, in da ya kuma umarci Hakimai da dagatai da su umarci al’ummar su tsaftace muhallin su da jikin su.

Alhaji Shehu Idris Shehu, ya kuma yi kira ga limamai na Masallatai dana Coci, dasu umarci mabiyan su da sukara  addu’a tare da kiyaye cunkusuwa waje daya don kaucewa yada cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!