Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Maryam Abacha ta tallafawa mabukata da kayan abinci

Published

on

Wani Malami a Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Yakubu Azare ya yi kira ga masu hannu da shuni dasu rinka tallafawa musu karamin karfi, musamman a wannan lokaci da ake zaman gida na dole, sakamakon annobar cutar Covid-19.

Farfesa Yakubu Azare ya yi wannan kiran ne a yayin da yake mika tallafin shinkafa da mai da wake ga mabukata, wanda gidauniyar tallafawa mabukata ta Maryam Abacha ta samar don ragewa marasa karfi radadin babu, musamman a wannan lokaci da gwamnati ta hana zirga-zirga na mako guda.

Farfesa Yakubu Azare ya ce idan mawadata na daukar dabi’ar taimakwa masu karamin karfi to kuwa tabbas za’a sami sauki matuka kan halin matsi da ake fuskanta.

Covid-19: Kungiyar tsaro ta Peace corp ta bada tallafi

Wasu da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su, tare da kira ga ragowar kungiyoyi da suma su rika bayar da ire-iren tallafin.

Gidauniyar ta Maryam Abacha ta tallafawa sama da mabukata dari biyu da karamin buhun shinkafa da wake da mangyada don rage musu radadi a wannan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!