Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Covid-19: Ganduje zai fara raba tallafin kayan abinci

Published

on

Kwamitin da gwamnatin jihar kano ta kafa na neman  taimakon  kan bullar cutar corona ya bayyana cewar tsare-tsare sun yi nisa domin ganin an fara gudanar da raban kayayyakin abincin da aka tara domin tallafawa al’ummar jihar Kano, a wani bangarena rage musu radadin halin da suke ciki game da annobar cutar Covid-19.

Farfesa Mahammad Yahuza Bello wanda shine shugaban kwamitin, kuma shugaban Jami’ar Bayaro dake nan kano, na ya bayyana hakan, jim kadan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan freedom radiyo wanda ya mayar da hankali kan tattaunawa da kuma Karin bayani kan kayayyakin da kwamitin ya samu zarafin Tarawa zuwa yanzu

Farfesa Mahammad Yahuza Bello ya kara da cewar an samu taimakon nau’in kayan abinci kimanin buhu dubu uku da dari uku kuma kayan amfani a bangaran kiwon lafiya da suka hadar da sabulun wake hannu sanitizer da darajar kudin say a kai naira miliyan dari uku da sabain da shida.

Shugaban kwamitin ya kuma kara da cewar za’a raba kayyayakin ga mutane dubu 50 a fadin jihar nan yadda ya kamata batare da samun wani tsaiko ba.

Mahammad Yahuza Bello ya kuma yi kira da dukkanin wanda yake da iko da ya tallafawa jama’a a dai-dai lokacin da mutane ke neman taimako, bayan da aka tilasta musu zaman gida don takaita yaduwar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!