Coronavirus
COVID19: Gwamnatin Jigawa ta bayar da umarnin a bude kasuwannin jihar
Gwamnatin Jihar jigawa ta bude dukkanin kasuwannin jihar da ke ci mako-mako, sai dai bisa sharadin za a rika bin dokokin da aka gindayawa ‘yan kasuwar.
Gwamnan jihar Alhaji Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi yayin wani taron manema labarai da fadar gwamnatin ta shirya a birnin Dutse.
Gwamnan ya kuma bukaci ‘yan kasuwar da suyi kokarin yin biyayya ga dokokin da aka gindaya musu.
Gwamnatin ta ce daga cikin sharuddan da aka gindayawa ‘yan kasuwar, akwai bayar da muhimmancin ga tsarin amfani da takunkumin rufe hanci da baki, da bayar da tazara da dai sauran dokokin da suka shafi yaki da cutar Covid19 mai saurin yaduwa.
Gwamnan yace an bude wannan kasuwanni ne sakamakon ci gaban da a’ke samu a yaki da cutar Covid-19.
Haka kuma badaru yace za’a kafa kotunan tafi da gidan ka, don hukunta duk mutanen da zasu yiwa dokar karan tsaye.
Gwamnan ya kuma ce duk kasuwar da a’ka samu basa bin wannan dokar kare kai to za a rufe ta.
Alhaji Badaru ya ce sun lura sosai kasuwanci da yan kasuwa sun shiga yana yi, kuma gashi kullum alkalaman masu kamuwa da cutar na raguwa, wadda hakan tasa suka dauki wannan mataki.
You must be logged in to post a comment Login