Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Sama da mutum 2000 aka yiwa gwajin cutar Covid-19 a Jigawa

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce mutum 2060 aka yiwa gwajin cutar Coronavirus tun daga lokacin da ta bulla a jihar zuwa yanzu.

Gwamna Alhaji Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Dutse.

Gwamnan yace cikin wancan adadi an samu mutane 283 da suka kamu da cutar inda tuni mutane 122 suka warke aka kuma sallae su yayin da mutum 8 suka rasu sakamakon  cutar.

Kan cigaban da ake samu game da yadda ake yaki da cutar gwamnan ya yabawa kwamatin yaki da cutar da kuma al’ummar jihar kan irin kokarin da kowanne bangare yayi.

Gwamna Badaru ya ce, tabbas al’ummar jihar sun bada hadin kai, ta wajan sanar da kwamati duk wanda suka gani da alammomin cutar da aka fada da kuma matakan da gwamnati ta gindaya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!