Labaran Wasanni
Cristiano Ronaldo ya zama gwarzan dan wasa firimiyar Ingila na watan Satumba
Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo ya lashe gwarzan dan wasa na watan Satumba a gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Ronaldo wanda ya dawo kasar Ingila a kakar wasannin da muke ciki bayan fafata wasa a kungiyoyin kasashen Sifaniya da Italiya ya doke dan wasa Mohamed Salah, Allan da Saint-Maximin, Antonio Rudiger, Joao Cancelo da kuma Ismaila Sarr
Ronaldo wanda ya koma filin wasa na Old Trafford a watan Agustan da ya gabata, bayan da ya fara buga wasa a watan Satumba a wasan da Manchester United tayi nasara akan Newcastle da ci 4 da 1.
Haka zalika dan wasan ya taba zama gwarzan dan wasan wata a kungiyar a lokacin tsohon mai horar da tawagar Sir Alex Ferguson.
Cristiano Ronaldo ya lashe gwarzan dan wasanne a karon farko tun a watan Maris din shekarar 2008.
‘Yan wasa Sergio Aguero (7), da Steven Gerrard ne suka lashe kyautar har sau 7 yayinda dan wasa Harry Kane ya lashe sau 6 sai kuma Cristiano Ronaldo ya lashe sau (5)
You must be logged in to post a comment Login