Coronavirus
Cutar Corona ta kashe mutane miliyan 3 a duniya – Jami’ar John Hopkins

Jami’ar John Hopkins da ke Amurka ta ce adadin wadanda suka rasa rayukansu sanadiyar cutar corona ya kai miliyan uku.
Wannan rahoton na zuwa ne a lokaci guda da cutar ke kara tsamari a kasashen Brazil, India da kuma Faransa.
A cewar jamira ta John Hopkins wadanda suka kamu da cutar a duniya yanzu sun zarce miliyan dari da arba’in.
Tuni dai hukumar lafiya ta duniya WHO ke ci gaba da shawartar shugabannin duniya da su ci gaba yin allurar riga-kafin cutar don dakile yaduwarta.
You must be logged in to post a comment Login