Kiwon Lafiya
Cutar Maleriya ta hallaka mutane dubu dari shida da goma sha tara a Najeriya – WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kashi 31 cikin dari na mutanen da zazzabin cizon sauro wato maleriya ya hallaka a duniya a bara yan Najeria ne.
Wannan na cikin rahotan maleriya da hukumar ta fitar tana mai jadda cewa duk da tasirin cutar Covid 19, da ake ci gaba da gani a halin yanzu zazzabin cizon sauran na ci gaba da halaka mutane a duniya.
WHO ta ce cutar ta hallaka mutane dubu dari shida da goma sha tara a bara bayan da ta kama mutane miliyan dari biyu da arba’in da bakwai adadin da ya zarce na shekarar 2019.
Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanon Ghebreyesus ya bukaci kasashen duniya da su tashi tsaye tare da kara kaimi wajen yakar cutar zazzabin cizon sauran, dan kare rayukan al’ummar su.
You must be logged in to post a comment Login